AMFANIN NONON RAƘUMI 13

 

Rakumi dabba ne me muhimmanci a yankunan hamada da yankuna masu tsananin yanayi. Baya ga fa’idar da rakuman dawa ke samarwa, nonon su wani abu ne mai kima da ake iya amfani da su ta hanyoyi da dama.

An bambanta madarar raƙumi ta hanyar abinci mai gina jiki mai wadata da bitamin da ma’adanai masu amfani ga jiki. Ya ƙunshi babban kaso na bitamin C, bitamin A, da bitamin B12, wanda ke haɓaka garkuwar jiki kuma yana inganta ayyukan tsarin juyayi. Har ila yau yana dauke da sinadarin iron, calcium da potassium, wadanda ke taimakawa lafiyar kashi, zuciya da tsoka.

 

Ɗaya daga cikin amfanin nonon raƙumi shine a ci shi a matsayin abincin lafiya. Ana iya shan nonon rakumi sabo ko kuma a yi amfani da shi don yin abinci da abubuwan sha masu daɗi da yawa, kamar su sherry mai sanyi, kayan zaki da kek. Ana kuma la’akari da madarar raƙumi a matsayin madadin madarar saniya mai kyau ga mutanen da ke fama da rashin haƙuri na lactose ko rashin lafiyar da ke tare da cin sauran kayan kiwo.

 

Baya ga amfani da abinci mai gina jiki, madarar rakumi kuma abu ne mai fa’ida a cikin kula da fata da gashi. Ya ƙunshi abubuwa masu ɗanɗano da kayan abinci masu gina jiki waɗanda ke ba da gudummawar haɓaka ƙwayoyin fata da haɓaka haɓakarta. Don haka yawancin kayan kwalliya da na fata sun ƙunshi madarar raƙumi a matsayin babban sinadari. Godiya ga wadataccen nau’in sa da kuma iya ɗora gashi, ana amfani da shi wajen yin kayan gyaran gashi, kamar shamfu da kwandishana, don samun lafiya da gashi mai sheki.

 

 

(1)CIWON SUGA.

 

Mai fama da larurar ciwon suga sai a samo: –

 

  • a) Nonon Raƙumi kofi daya.
  • b) Tirmis Baladi, cikin ƙaramin cokali
  • c) Garin Hulba, karamin cokali
  • d) Hubuwbul liƙah ƙaramin cokali
  • e)Markadadden bitter lemon ƙaramin cokali.

 

Sai a kaɗa su a cikin nonon, sai a sha kofi daya da safe

kofi daya da yamma tun kafin a ci abinci da awa daya,

ma’ana idan an sha maganin sai an samu awa đaya a tsakani sannan za a ci wani abu.

 

(2) CIWON CANCER

 

Wanda yake da wani ciwo da ya shafi cancer to

sai ya yi kokarin jarraba wannan maganin:

Zai rika shan kofi daya na nonon rakumi da safe da yamma amma tun kafin ya ci wani abu da awa daya. Ma’ana, ba zai ci wani abu ba zai sha maganin. Idan kuma ya sha maganin to sai ya

Samu awa daya a tsakani, sannan zai ci wani abu. Za

a yi haka a jere ba fashi tsawon kwana arba’in da

biyar. Sannan duk sanda ya sha wannan nonon to zai

sha shayin lipton ba madara cikin babban kofi tare da rabin kofi na fitsarin rakumi sai ya gauraya ya rika

sha tsawon adadin kwanakin.

 

Sannan shi kansa fitsarin rakumin idan an

tafasa shi da ruwa ana yin shayi lipton ba madara

ana sha, to magani ne sadidan

 

(3) CIWON SANYI

 

Idan mutum yana fama da ciwon sanyi, to sai ya

yi kokarin hada wadannan mahadđan, insha Allahu

zai fitsarar da sanyin da yake takura masa a jikinsa.

 

a)Nonon Raƙumi kofi daya

b) Kanunfari karamin cokali

c) Irƙu Dahab, ƙaramin cokali.

 

To sai ya hada ya sha kofi daya da safe, tun

kafin ya ci wani abu. Sannan kofi daya da yamma,

kofi daya da daddare. sharaɗi shi ne, duk sanda aka sha ba

za a ci komai ba sai an samu awa daya da rabi (1/2

hrs) a tsakani sannan za a ci wani abu.

 

(4) FITAR RUWA MAI WARI A GABAN MACE

 

Sanyi na iya sanya mace ta rika fitar da wani

ruwa mai wari, to maganin

wannan matsala shi ne, sai ta samu fitsarin rakumi

mai dama sai ta tafasa shi, sai ta rika shiga cikin

ruwan tana zama a ciki zuwa rabin awa, sannan ta fito. Za ta rika yin haka sau daya a rana, tsawo satin daya.

 

(5) RASHIN FITAR JININ HAILA

 

Sai ta samu madarar nonon rakumi ta sha kofi

daya da safe kofi daya da yamma, to in sha Allahu

za ta samu saukin lamarin.

 

(6) MAGANIN ƘURAJEN PIMPUS

 

Duk wanda kurajen pimpus suka dame shi suka

6ata masa fuska da fata, to sai ya samu madarar

nonon rakumi ya riƙa shafawa a kai, sannan kuma

yana shan kofi daya da safe da yamma, tsawon sati

biyu. To insha Allahu fatarsa za ta yi kyau, duk wasu

bakaken kuraje masu fesowa a jiki za su bace su

warke, fata za ta yi kyau da haske.

 

(7) ƘAIƘAYIN FATA

 

Duk wanda yake fama da soshe-soshen fata, da

karce-karcen fata, to, sai ya yi kokarin hada

wadannan mahadan:

 

a)Nonon Raƙumi

b)Hububul liƙahu

c) Fitsarin Rakumi

 

Da farko kullum zai sha nonon rakumi kofi uku

tare da Hububul Lika’hu karamin cokali a rana daya, safe da yamma da daddare, to amma tun kafin a ci

wani abu ake sha. In ma an sha sai an samu rabin

awa a tsakanı, sannan za a ci wani abu.

To, bayan ya sha wannan hadin, sai ya samu

fitsarin rakumi tare da man zaitun ya hada waje daya

ya rika shafawa a jikinsa sau uku a rana.

 

(8) ZAFIN FITSARI

 

Wanda yake fama da ciwon fitsari wato yana

fitsari da kyar, wani lokaci yana jin kamar ana kona

gabansa, to sai ya yi amfani da fujul wato ya

tafasa shi a cikin madarar Nono Raƙumi yana ci da safe tun kafin ya ci wani abu.

Abu na biyu mutum zai iya amfani da wadannan

mahaɗan:

 

a)Nonon rakumi kofi daya

b)Shammar karamin cokali

c) Halful Barri, ƙaramin cokali

 

Da farko idan an samu kofi daya na nonon rakumi to sai a zuba karamin cokali na garin Shammar sai a shanye shi sai kuma karamin cokali na garin

Halful Barri shi kuma tafasa shi za a yi a ruwa a rika

sha. Za a rika yin haka sau uku a rana amma sai an

ci abinci za a rika sha.

kafin ya ci wani abu.

 

(9) FITSARIN JINI

 

Mahadan su ne:-

1) Nonon Raƙumi

2) Kanin fari karamin cokali

3) Irƙu Dahabu rabin karamin cokali

 

Sai a zuba su a cikin nono a juya a sha safe da

yamma da daddare tun kafin a ci wani abu, idan

kuma an sha maganin to kar a ci wani abu a lokacin

har sai an samu rabin awa ½hr.

 

(10) CIWON SHAWARA

 

Mai ciwon shawara sai ya lazimci shan ruwa

kofi daya da safe tun kafin ya ci wani abu, sannan

kuma sai ya sha Nonon Raƙumi kofi daya tare da cin

kayan marmari kamar su ayaba gwanda, mangwaro

tufa, da dai sauransu

 

(11)DOMIN SAMUN ƘWARIN ƘASHI

 

Sai a samu wadannan mahadan:

a)Nonon rakumi

b)Fitsarin rakumi

c)Man Kafur

d)Man Na’a-na’a.

 

Da farko duk sanda ake cin abinci safe da rana da na dare, to sai a sha kofi daya na nonon rakumis annan kuma sai a samu fitsarin rakumi sai a zuba man kafur da man Na’a-na’a, sai a juya shi sosai a riƙa shafe gaba dayan jiki da shi. Za a yi haka sau uku a yini.

 

(12) RAUNIN JI NA KUNNE

 

Mai fama da raunin ji na kunne, to sai ya yi amfani da auduga mai kyau sai ya jika ta da fitsarin rakumi, sai ya sa audugar a kunnuwansa tun daga yamma har zuwa wayewar gari, sai ya cire. To insha Allahu zai ji yadda kunnensa zai kasance dangane da ji sosai.

 

(13) MAGANIN DASKAREWAR JINI A JIKIN MUTUM

 

Mai fama da matsalar daskarewar jini, sai a samu

 

1) Nonon Raƙumi kofi ɗaya

2) Garin Habbur Rashad karamin cokali

3) Bizru Kattan, wanda aka daka shi, karamin cokali.

4) Garin citta mai laushi, karamin cokali

5) Hubbu Likahu karamin cokali.

 

Da farko idan aka samu nonon, to sai a zuba wadannan mahadan a ciki, sai a sha kofi đaya da safe tun kafin a ci wani abu, sannan bayan an sha za a samu kamar rabin awa, sannan za a iya cin wani abu. Haka ma da yamma za a sha bayan an sha a sami rabin awa sannan a ci wani abu.

 

Read more 

 

 

Leave a Comment