Maganin Hausa

Ingantaccen Sahihin Maganin Istimna’i 2024

Waraka daga cutar istimna’i yadda zaka daina da kuma yadda zaka magance matsalar cikin sauki wannan maganin yana aiki sosai saboda haka a tsaya a karanta a natse.

Gabatarwa Ganeda Maganin Istimna’i 2024

Magani wanda aka jarraba yana aiki dari bisa dari sannan wannan maganin da zamu baku anan babu irinsa, sannan kuma kafin kasan maganin istimna’i ya kamata kasan wasu abubuwa game da istimna’i wanda ta hakan ne kadai zaku iya kiyayewa da magance wannan matsalar.

 

Da farko dai ya kamata musan menene shi istimna’i wanda a turance ake kira masturbation wato yin amfani da hannu domin gamsar da kai, wannan bala’i ne wanda ya mamaye samarin mu a yanzu wanda ana samu har cikin maauratan ma zaka samu mutum yana da aure amma kuma yana aikata wannan mumunan dabiaar wanda kuwa hakan ya samu asali ne sakamakon yana yi tun kafin yayi aure.

Istimna’i ana kiranshi zinar hannu wato mutum ya rika wasa da azzakarin sa har ya gamsar da kansa, ya fitar da maniyi wanda hakan shine zai bashi damar yaji dadi kamar yayi jima’i saidai kuma wannan akoi hatsari mai girma.

Abubuwan Da istimna’i Yake Haifar Wa Mutumin Da Yake Aikatashi

Ingantaccen Sahihin Maganin Istimna’i 2024

 

 

 

 

 

 

 

A wannan gabar ana samun wasu wadan da suke ikirarin cewa Istimna’i yana da amfani wanda wannan kwata kwata karya ce saboda kuwa Istimna”i a Addinance ma babu kyau kuma duk abunda addininka ya hanaka dole idan kayi duba zaka ga akoi illa sosai gameda hanin da aka maka wannan ya sanya wasu kullum suke bibiyar wanda zai halatta musu Istimna’i saboda suci gaba da aiwatar wa wanda sai sunyi nisa aciki zasu zo su fara ganin illolinshi zai rika bayyana musu kara ra a fili wanda hakan zai sanya su dana sanin aikatawa.

 

KARANTA: Maganin Karfin Maza Da Jima’i Da Kankan Cewar Gaba 2024

Ingantaccen Sahihin Maganin Istimna’i 2024

Ga wsu daga cikin abubuwan da Istimna’i ke haifar wa wanda kuwa koda baka ganshi yanzu ba zaka ganshi nan gaba muddin baka dena wannan kazamtar ba.

 1. Saurin Kawo maniyi
 2. Kankancewa gaba
 3. Ciwon jiki
 4. Lalata kwayar halitta
 5. Rage karfin ido
 6. Lalata azzakari
 7. lalata maran namiji

 

 1. Saurin Kawo maniyi: Wato wannan yana faruwa ne a lokacin da zaka yi jima’i da zaran ka fara nan take zakaji har ka kawo bazaka gamsar da iyalinka ba sannan ruwan maniyyin da zai fito bashida karfi
 2. Kankancewa gaba: Zai lalata maka azzakari wanda hakan zai sa azzakarinka ya kankance koda kuwa kana bukatar yin jima’i azzakarin bazai tashi ba sannan koda ya tashi ma bazai dade a mike ba saboda ka saba masa da istimna’i.
 3. Ciwon jiki: Kullum da safe zakaji kamar and dakeka idan ka kwanta barci bakason tashiwa saboda kasala wannan yana faruwa ne saka makon istimna’i da kakeyi.
 4. Lalata kwayar halitta: Zai hanaka haifuwa koda kuwa ace ka yishine a lokacin da kake yaro idan kazo kayi aure istimna’i zai hanaka haifuwa kwatakwata saboda zaka gamu da Low Sperm wanda wannan zai sanya ruwan maniyyinka zaiyi kadan bazai kaiga shiga mahaifa har a samu ciki ba.
 5. Rage karfin ido: Tabbas likitoci sun tabbatar da cewa istimna”i yana haifar da matsalar gani tun kana karami zaka bukaci aiki da eyeglass saboda wannan istimna’i ya lalata maka kwayar ido.
 6. Lalata azzakari: Zai kashe maka gaba completely ta yadda haka kawai zakaji gabanka yana fidda ruwa sannan bazai rika tashi ba koda kuwa ace shaawarka ta motsa.
 7. Lalata maran namiji: Wato zai sanya maka matsalolin mara yoyon fitsari da fitsari mai zafi sannan zai tara maka macecen maniyyi a mararka.

Wadannan kawai mun kawo su ne saboda kuwa sune zasu iya bayyana maka amma kuma akoi wasu abubuwan da yewa wanda wannan Istimna”i zai haifar maka a rayuwarka.

Hukuncin istimna’i a Musulunci 2024

Istimna’i wannan ana kiranshi da zinan hannu saboda mutum zai rika wasa ne da azzakarinsa ko kuma farjinta saboda ya fitar da maniyyi wanda fitan maniyyi din shine zaisa mutum yaji dadi sannan yaji baya bukatar mace saboda ya riga ya fitar da shaawar dake jikinsa.

 

Masu Istimna”i sukanyi amfani da abubuwa da dama wurin ganin cewa sun fiddo maniyyi saboda jin dadinsu misali:

Ingantaccen Sahihin Maganin Istimna’i 2024

 • Sabulu

 •  Istimna’i Na Waya

 • Kallon fina finan batsa

Wadannan sune kadan daga cikin abubuwan da ke taimakawa masu Istimna”i domin gamsar da kansu,

 

Istimna’i a musulunci haramun ne saboda Allah yace bashi halatta ka biyawa kanka bukata idan bata hanyar aure ba ko ta hanyar kuyanga a lokacin bayi kenan.

 

Saboda haka duk wanda zai ce maka ai yakamata ka rika yi domin gujewa zina gaskiya wannan kwatakwata ya jefaka ne cikin matsala saboda kuwa wannan zai haifar maka mummunan matsala wanda zai iya zama sanadiyar lalacewar rayuwarka.

ingantaccen maganin istimna”i Na Gargajiya Da Bature 2024

Domin magance matsalar Istimna’i dole sai ka daina shi wannan shine matakin farko muddin baka daina shi ba to babu wani chanjin da zaka gani, ga hanyoyin da zaka bi domin daina aikata Istimna’i.

 

 • Ka daina kallon duk wani abunda zai motsa maka sha’awa.
 • Ka daina kwana kai kadai a daki, sannan ka daina kasancewa kai kadai.
 • Ka rika azumi sannan ka samu abunda zaka rika shagala dashi.
 • Ka rika yin sallah akan lokaci

 

Insha Allah wadannan sune abubuwan da zaka gabatar domin kaucewa wannan mummunar abun saboda kuwa idan baka daina shi ba magani bazaiyi aiki ba.

 

Maganin Istimna’i A saukake:

 

Ya dan uwa kasan cewa babu sahihin maganin Istimna’i saboda haka yewanci zakaga mutane suna tallar maganin istimna’i wanda yewanci wadannan magunguna bazasu kashe Illar da istimna’i ya maka ba abu mafi kyau shine ka daina shi bayan ka daina sai kabi wadannan matakan kamar haka.

 

 • Ka rika cin abinci wanda bashida maiko
 • Ka rika shan kankana akai akai wannan shine babba kullum kafin ka kwanta kasha kankana.
 • Ka rika motsa jikinka da safe kullum kadaina zama da kasala

 

Ga wani hadi shima yana aiki dari bisa dari saidai yana bukatar dagewa domin samun abubuwan hadin.

 • Nonon saniya (madara)
 • Saffron (Crocus sativus) Wannan kuma yaren indianci ne wani abune da ake samunshi akan flower.

Zaka daka Saffron sannan ka tankade saika zubashi cikin Nonon saniya ka rika sha kullum idan zaka kwanta barci insha Allah zaa dace.

 Read more

Leave a Reply

Back to top button